Mutane 3 da suka fi kowa basira a duniya
Kwanaki Legit.ng ta kawo maku jerin wadanda su ka fi kowa kudi a Duniya irin su Bill Gates mai Dala Biliyan 86. Yanzu kuma mun kawo wani jerin na wani babi
Kwankwalwa dai baiwa ce kurum daga Ubangiji ba kokari bane ke bada ta. A kan auna kaifin kwakwalwa ne da mitar IQ. Yanzu haka dai an gano wadanda su ka zarce kowa kaifin basira a Duniya, a cikin jerin kuwa har da wani ‘Dan Najeriya. Legit.ng ta kawo maku sunayen su:
1. Terrence Tao
Harsashe ya nuna cewa duk fadin Duniya babu mai kwanyar Mista Tao wanda rabi Ba’Amuruke ne kuma dayan barin sa Dan kasar Sin wanda aka haifa a Australia. Makin sa na IQ ya fi na kowa inda yake da 230. Tun yana shekara 20 ya gama Digiri na uku yanzu kuwa Farfesa ne tun yana dan shekara 24.
KU KARANTA: Masana sun ce akwai alamar tambaya a Tarihin Bayajidda
2. Chris Hirata
Christopher na da makin IQ har 225 shi ma wani dan baiwan ne wanda ya kammala Digiri na uku watau PhD tun yana dan saurayin sa. Yanzu haka Malamin Jami’a ne a Birnin Kalifonia.
3. Kim Ung-Yong
Kim Injiniyan gina-gine ne kuma mutumin kasar Koriya wanda tun kafin ya shekara a Duniya ya fara magana. Yana da makin IQ 210 don haka kuwa yana cikin masu basirar Duniya
KU KARANTA: Kannywood: An kammala shirin wani babban fim
A cikin dai wannan jeri akwai wani Dan Najeriya da ya zo cikin sahun 10 na farko mai suna Philip Emeagwali. Emeagwali ba dai basira ba, an haife sa ne Garin Akure ko dai dai Inyamuri ne.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ta koka da rashin 'ya 'ya a Duniya
Asali: Legit.ng