Ana neman tsohon Gwamnan Jihar Kebbi bisa zargin cin wasu kudi
Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Usman Saidu Nasamu Dakingari ya ga ta kan-sa yayin da Majalisa ta ke neman sa domin yayi mata wasu bayani
Majalisar dokoki na Jihar Kebbi na neman tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Saidu Usman Dakingari domin yayi mata bayanin yadda aka tsula kudin aikin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da aka yi a lokacin sa.
Majalisa ta dai ba tsohon Gwamnan makonni 3 ne rak ya hallara a gaban ta domin jin yadda kwangilar Naira Biliyan 18 ta kara tashi sama da kusan Naira Biliyan 6 da ‘yan kai. Yanzu dai Majalisar ta ba ‘yan kwangila umarni su maido wadannan makudan Biliyoyi da aka cusa.
KU KARANTA: EFCC tayi wani mugun damka a Kaduna
An dai kafa kwamitin bincike na musamman a Majalisar kamar yadda Legit.ng ke samun rahoto wanda mataimakin kakakin ta Muhammadu Buhari Aliero ke jagoranta. Tuni dai an zauna da ‘yan kwangilar har kuma an gano yadda aka tsula kudin kwangilar da kusan Biliyan 10.
Haka kuma Alkali Nasiru Saminu na Babban kotun tarayya da ke Kano ta yankewa wani shugaban makaranta watau Hedimasta hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da wani zabi ba bayan an same sa da laifin kwanciya da kananan yara ‘yan makarantar har 2.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wani mutumi ya tsinewa shugabannin Najeriya
Asali: Legit.ng