Allah daya gari bam bam: Za'a daure ka har ka mutu idan ka yanka sanuwa a nan
- Jihar Gujarat da ke yammacin India ta zartar da wata doka da za ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan duk mutumin da aka kama da laifin yanka saniya
- A karkashin dokar kare hakkin dabbobi, duk wanda aka samu da laifin jigilar naman shanun zai sha daurin shekara goma
Legit.ng ta tattaro cewa akasarin 'yan kasar Indiya suna daukar saniya da babban matsayi, kuma jihohi da dama sun haramta kashe shanu.
Sai dai gyaran da aka yi wa dokar a Gujarat na nufin ita ce jihar da ta fi daukar tsattsauran mataki kan duk wanda ya kashe shanu.
KU KARANTA: Nafisa Abdullahi bata yadda a maido Rahma Sadau fim ba
Haka kuma za a ci tara mai tsanani ta $771 kan mutumin da aka kama da laifin kisan ko yanka shanu.
Ministan Gujarat ya shaida wa manema labarai cewa saniya wata alama ce ta al'adun India, yana mai cewa an dauki matakin ne bayan an tuntubi al'umar jihar.
Vijay Rupani ya sha jaddada cewa za a yanke hukunci mai tsauri kan duk mutumin da aka kama da laifin kashe saniya.
Za a soma aiwatar da dokar ce ranar Asabar.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Shi kuwa wannan cewa yayi yan siyasar Najeriya sun cancanci hukucin kisa
Asali: Legit.ng