An aika wasu mutane gidan yari a dalilin lalata da maza
Kotu ta bada umarni a jefa wasu mutane gidan maza a Kano a dalilin sha’awar maza da su ke yi. Wannan dai ba karamin laifi bane a Najeriya da ma kasashe da dama
Kotun majistare da ke Sakatariyar Audu Bako a Jihar Kano ta bada umarni a jefa wasu mutane 2 cikin kurkuku a dalilin sha’awar maza da su ke da shi. Wadannan mutane dai sun ce ba su ga laifin yin hakan ba kuma su ka bayyanawa kotu cewa su na da gaskiya.
Abdullahi Muhammad dan shekara 50 da kuma Musa Garba mai shekaru 20 a Duniya sun bayyana cewa ba su aikata wani ba daidai ba don su na sha’war maza ‘yan uwan su. Mai karar yace ba sau daya ba kenan ana kama wadannan mutane suna aikata wannan babban laifi a tsakanin su.
KU KARANTA: Wani Fasto ya kai ziyara wurin Gwamnan Kaduna
Alkali mai shari’a Mohammed Jibril ya nemi a daure wadannan mutane har sai wata mai zuwa sannna a cigaba da shari’a. A Najeriya dai muddin aka kama mutum da wannan laifi zai yi shekaru 14 ne a gidan yari.
Kwanaki wata Kungiya mai suna Youth Hub Africa ta kira taron wayar da kai a game da kar hakkin yara na sama masu ilmi da kare su daga fyade ko wani abin da zai cutar da su.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Hukumar DSS sun yi ram da wasu
Asali: Legit.ng