‘Musabbabin rigima ta da gwamnan jihar Bauchi’ – Dogara

‘Musabbabin rigima ta da gwamnan jihar Bauchi’ – Dogara

Kaakain majalisar wakilan Najeriya onorable Yakubu Dogara ya bayyana dalilin daya sa basa ga maciji da gwamnan jihar Bauchi Muhammed Abubakar.

‘Musabbabin rigima ta da gwamnan jihar Bauchi’ – Dogara
Dogara

Dogara yace shi fa abinda daya hada shi takun saka tsakaninsa da mai girma gwamna Muhammed Abubakar bai wuce rashin tabuka komai ga talakawan jihar ta Bauchi ba, inda yace har yanzu gwamnan ya kasa samar da romon dimukradiya ga al’ummar jihar ta Bauchi.

KU KARANTA: Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU na shirin shiga yajin aikin gama gari

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da manema labaru ciki har da majiyar Legit.ng a ofishinsa a ranar Talata 28 ga watan Maris inda yace “Ba zan taba goyon bayan duk wanda ba zai samar ma jama’a romon dimukradiyay ba, wannan itace matsala tad a gwamnan Bauchi.

“Duk wanda ke kokarin sauke nauyin dake kansa, kuma yana cika alkawurran daya daukan ma jama’a, tabbasa wannan shine mutumi na, kuma abokin aiki, amma muddin ya zaman ka gaza kan sauke nauyin da ke kanka, ba zamu taba zama wuri daya ba, don idan lokacin kin dillanci yazo, kaga bana nan.

“Wannan ne matsalar da muke samu, ba wai batun bana son yin aiki tare da shi bane, zan iya aiki da duk wanda manufarsa itace kawo ma al’umma cigaba, amma idan ba haka, ba zan yaudareka in ce ina tare da kai ba, alhali na san bana tare da kai,” inji Dogara.

Dogara ya cigaba da fadin dalilinsa na dauke kafa daga jihar Bauchi, inda yace: “Zan iya zuwa gida ko yaushe kuma a kowane lokaci.. don ko a watan Disamnar bara sai da naje gida, kuma nan bada dadewa ba zan sake komawa.

“Don haka ina so inyi amfani da wannan dama don in shaida ma jama’an jihar Bauchi cewa zani gida, domin kawar da shakkar masu tunanin wani nayi gudun hijira ne,” inji Dogara.

Dangantaka tayi tsami ne dai tun lokacin da sojojin baka suka fara bayyana cewar Kaakakin majalisa Yakubu Dogara ya fara sunsunan kujerar gwamnan jihar, wannan yasa har aka smau rarrabuwar kai a majalisar dokokin jihar tsakanin bangaren gwamna da magoya bayan Dogara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kana dana sanin zaben shugaba Buhari? saurari ra'ayoyin jama'a anan:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel