LABARI DA DUMI-DUMI: An saki tsohon gwamnan jihar Adamawa daga gidan yari
- An saki tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala James Ngilari daga gidan yari.
- Babbar kotun 1 na Yola ta bayar da belin bisa wani rahotona likita kan kiwon lafiyarsa.
Tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Bala James Ngilari, wanda aka bayar da belin a kan kiwon lafiya, bayan ya daukaka kara a kan laifin cin hanci da rashawa da ya sa aka yanka masa daurin shekaru biyar a gidan yari.
Legit.ng ta ruwaito cewa controller na gidan yari shiyar Adamawa, Mista Peter Tenkwa ya tabbatar da wannan labari a ranar Laraba, 29 ga watan Maris a Yola.
Controller ya bayyana cewa an saki tsohon gwamnan ne "ba tare da sani na ba".
Justice Nathan Musa, alkalin babban kotun 1 a Yola ya ba da belin Ngilari a ranar Litinin, 27 ga watan Maris har zuwa lokacin sauraren daukaka karar.
Sanadiyar ba da belin tsohon gwamnan ya biyo bayan wani rahoto likita, wanda ya nuna cewa ya na fama da rashin lafiya mai tsanani kuma zai bukaci tafiya kasan waje don nemo kulawa ta musamman.
Amma Tenkwa ya gaya wa manema labarai cewa ya na jiran umurnin kotun kafin ya tuntubi bangaren shari’a ta hukumar don neman shawara kan al’amarin, a wannan lokacin ne mataimakin Controller mai lura da gidan yari na Yola, Abubkar Abaka, ya gaya masa cewa ai tuni aka saki Ngilari.
KU KARANTA: Rikicin majalisa da Ibrahim Magu: Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani
Ngilari ya kasance a matsayin gwamnan jihar Adamawa daga watan Oktoba 6, 2014 zuwa matan Mayu 29, 2015, bayan tsigewar mukaddashin gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri da wata babbar kotun da ke birnin Abuja ta yi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon tsohon shugaban NNPC a lokacin shari'a a kotu kan wasu miliyoyin kudi da aka gano a gidansa
Asali: Legit.ng