Mahaifiyar Janar Ishaya da Musa Bamaiyi ta rasu bayan shekaru 99 a duniya
Allah ya wa mahaifiyar Janar Ishaya Bamaiyi da Janar Musa Bamaiyi rasuwa bayan ta shafe shekaru 99 a duniya.
Legit.ng ta samu rahoto cewa Allah ya wa mahaifiyar Janar Ishaya Bamaiyi da Janar Musa Bamaiyi ta rasu bayan ta shafe shekaru 99 a duniya.
Janar Musa da Ishaya Bamaiyi sun kasance 'yan'uwa jini daya. Dukansu sun yi ritaya a aikin soja a matsayin janar. Wadannan, watakila, shi ne kawai abubuwan da suke dauke da a matsayin ‘yan’uwa.
Musa ne babban wa a tsakanin mazan biyu, kuma shi ne aka fi tsoro a lokacin da ya ke shugabancin hukumar NDLEA.
Ishaya kuma ya kasance babban hafsan sojoji, (COAS) a lokacin da dan'uwansa ke rike da NDLEA.
KU KARANTA: Ko kasan abin da Bishof Azogu ya ce zai faru idan Buhari ya mutu?
Ita kadai ce a Najeriya da ta samu Janar biu a lokaci daya kuma masu kokari wayanda suka sadaukar da rayuwar su ga aikin kasar.
Allah ya ba iyalanta hakuri.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon wata mata inda ta ke kokawa yadda ta rasa yara 4 sanadiyar rushewar gidajensu da gwamnatin jihar Legas ta yi.
Asali: Legit.ng