‘Ýan Boko Haram sun tilasta min kashe mutane 13’ – inji wani yaro mai shekaru 17

‘Ýan Boko Haram sun tilasta min kashe mutane 13’ – inji wani yaro mai shekaru 17

Wani karamin yaro dan Boko Haram mai shekaru 17 ya bayyana yadda shuwagabannin kungiyar ta’addancin suka tilasta masa kashe mutane 13 a cikin kungurmin dajin Chikingudu dake karamar hukumar Kala-galbe na jihar Barno, inda suke tsare da shi har tsawon shekaru 3.

Yadda yan Boko Haram suka tilasta ma ƙaramin yaro kashe mutane 13 (Hoto)
'ƙaramin yaron daya kashe mutane 13

Kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito jami’n hukumar tsaro ta farin kaya, wato Civil defence ne ta kama yaron a lokacin da shugabannin kungiyar suka aike shi liken asiri zuwa cikin garin Maiduguri.

Yaron ya bayyana ma jami’an, civil defence cewa manyansa ne suka aike shi garin kasuwar Monday da kasuwa Kwastam dukkaninsu a cikin garin Maiduguri don ya yo musu liken asiri.

KU KARANTA: Abubakar Shekau na raye - Gwamnatin tarayya

“A garin Marte yan Boko Haram suka sace ni a shekarar 2013, inda suka wuce damu dajin Chikungudu a karamar hukumar Kala balge, shekaru na uku a hannunsu, ina tsare a dajin Chikungudu, a cikin wannan shekarun na kashe mutane 13 a waurare daban daban.

“Da farko na kashe mutane a dajin Chikungudu inda suke tsare damu, suna tilasta mana kisan kai musamman idan sun dawo daga kai hare hare, a haka suka sani na kashe mutane 5. Da fari na yi taurin kai, amma sai suka yi barazanar kashe ni, don haka dole nayi musu biyayya. Daga bisani sai suka sake kawo mutane 3, suka in kashe su, kuma na kashe su.

“Na biyu kuma, a wani kauye da ake kira Burssari ne, suka kawo min mutane 5 wai in kashe su, kuma na kashe su. shekaruna uku tare da yan ta’addan, rayuwar mu ta lalace. Sun bamu horo kan yadda zamu warware tare da hada bindigar AK-47,” inji yaron.

Yaron ya bayyana cewa akwai kananan yara sa’anninsa sama da 500 da aka shigar dasu kungiyar Boko Haram a dajin Chikungudu.

Shugaba hukumar NSCDC reshen jihar Borno Ibrahim Abdullahi yace sun samu nasarar kama yaron ne a kusa da sansanin uan gudun hijira na Bakassi, dake garin Maiduguri. Abdullahi yace an gano iyayen yaron a sansanin na yan gudun hijiran.

“Zamu mika wanda ake zargin zuwa ga hannun jami’an rundunar soji don cigaba da bincike akansa.” Inji Abdullahi.

A kwananan sai da jaridar Legit.ng ta kai ziyarar gani da ido zuwa sansanin yan gudun hijira dake Abuja don ganin halin da suke ciki, sakamakon halin da rikicin Boko Haram ya jefa su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon mutanen da suka sha daga harin Boko Haram

Asali: Legit.ng

Online view pixel