Abubakar Shekau na raye - Gwamnatin tarayya
Daga karshe gwamnatin tarayya ta amince da cewan shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau na raye har yanzu.
Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, ya bayyana hakan a ranar Talata, 28 ga watan Maris, jim kadan bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan ma’aikatar sa a fadar shugaban kasa, Abuja.
Dan Ali yayi bayanin cewa kama shugaban yan ta’addan yayi ma hukumomin tsaro wahala saboda yan ta’addan na rufe fuska don boye kammaninsu da kuma dauke hankulan mutane, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Buhari ya tsige daraktocin tarayya 5
A halin da ake ciki, ministan ya bada tabbacin cewa za’a kama Shekau nan bada jimawa ba.
Yace duk wanda Allah yaba daman ziyartan dajin Sambisa zai san cewa an yi nasara a kan yan Boko Haram.
Legit.ng ta rahoto inda, Dan Ali ke yace hukumomin tsaro na kasar zasu ci gaba da mamaye dajin Sambisa, tsohon sansanin yan ta’addan, don gano inda Shekau yake.
“Na yarda da cewan komai lokaci ne. ya dauki kasar Amurka shekara bakwai zua goma kafin ta kama Bin Ladan. Don haka, zamu kama Shekau nan bada jimawa ba.
“An kakkabe hedkwatar yan ta’addan. Shi (Shekau) na neman hanyar gudu.
“Babu mamaki yana nan boye a bangare daya na dajin Sambisa wanda muka mamaye a yanzu.
“Mun bude gurin. Muna amfani da gurin a mastayin gurin horo. Injiniyoyin hukumar soji zasu bude hanyoyi sannan kuma zamu kewaye dajin don sanin inda Shekau yake,” cewar sa.
KU KARANTA KUMA: Ba za mu sake bari ‘Yan ta’adda su kwace wani yanki na kasar nan ba – Inji Buhari
Da aka tambaye shi kan dalilin da yasa gwamnati tayi ikirarin cewa an kashe Shekau a baya, ministan yace barda kammani da yan ta’addan keyi ne ya haifar da haka.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Bidiyon wata yarinya da aka ceto daga rikicin Boko Haram a Arewa maso gabashin kasa:
Asali: Legit.ng