Idan ka ji abin da wani Lauya yayi sai ka rike baki
- Wani Lauya a kasar Kenya ya maka mutanen kasar Israila kara a Kotu
- Lauyan yace mutanen Isra’ila ne su ka kashe Yesu Almasihu
- Wannan abu dai ya ba mutane mamaki
Wani Lauya mai suna Dola Indidis a kasar Kenya ya maka kasar Isra’ila a babban Kotun Duniya da ke Birnin Hague kara inda yake zargin mutanen kasar da kashe Yesu Almasihu wanda Musulmai su ke kira Annabi Isa kuma Kiristoci su ke bauta masa.
Lauyan yace kashe Annabi Isa da aka yi a bisa kan sarka ba daidai bane, zallar zalunci ne wanda ya saba hakkin bil adama. Babban Lauyan ya nemi a hukunta kasar Israila da kuma Sarkin Daular Rumawa a wannan lokaci da ma kasar Italiya. A littatafan Kirista wannan abu ya faru sama da shekaru 2000 da su ka wuce.
KU KARANTA: Gwamna El-Rufa'i ya rubuta wasika ga shugaban kasa
Sarakunan Daular Rumawa ne dai su ka yanke hukuncin kashe Yesu wanda ake kira Jesus a wancan lokaci. Wannan babban Lauya na kasar Kenya yace dole a sake binciken shari’ar da aka yi don kuwa ba a bi ka’idar kotu ba.
Mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi kira da Fastocin kasar nan su ji tausayin talakawan da ke fama a cikin wannan yanayi su saida jiragen su. Reno Omokri wanda shi ma Fasto ne yace Yesu Almasihu ya rika ciyar da Bayin Allah a lokacin sa.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng