Fulani makiyaya sun kai hari gidan yarin jihar Binuwe, an kashe mutum guda
Hukumar kula da gidajen yarin jihar Binuwe ta tabbatar da wani hari da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kai mata a sabuwar gonar gidan yarin dake Jato-Aka, inda suka hallaka mutum daya mai suna Tersoo Agidi.
Kaakakin hukumar kula da gidajen yarin, Stephen Nwanchor ne ya tabbatar da kamfanin dillancin watsa labaru, NAN, a garin Makurdi, babban birnin jihar Binuwe, inda ya shaida mata cewar an kai harin ne a ranar Asavar 25 ga watan Maris.
KU KARANTA: Neman sulhu: El-Rufa’i ya gana da jiga-jigan APC jihar Kaduna (Hotuna)
Sai dai mista Nwnchor ya tabbatar ma majiyar Legit.ng cewa harin ba shi da alaka da kokarin fasa gidan yarin don kwato mazauna gidan.
“Wannan sabuwar gonar gidan yarin mu ne da aka kaddamar da shi a watan Janairun 2017, Makiyayan sun kai hari wajen, kuma sun lalata dukiyoyi, tare da hallaka wani mazaunin gidan yarin Tersoo Agidi.
“A yanzu mun kwashe dukkanin mazauna gidan yarin zuwa garin Gboko, kafin a kammala gudanar da bincike. Ba zamu yi sakwa sakwa ba, kuma shugaban hukumar kula da gidajen yarin ya sanar da dukkani sauran hukumomin tsaron kasar nan,” inji Nwanchor
Kaakakin hukumar yace suna gudanar da bincike don tabbatar da musabbabin dalilin kawo harin, sa’annan ya tabbatar da cewa basu kama kowa ba zuwa yanzu.
Nwanchor yace hukumar su ta kara damarar tsaro a yankunan gidan yarin da duk sauran ofisoshinsa, don haka yake bayyana ma jama’a da kada su shiga rudani, babu wata matsala.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga biidiyon rikicin Fulani makiyaya da manoma a kudancin Kaduna
Asali: Legit.ng