Aiki na kyau! Kunji sabon farashin dala a yau?
Babban Bankin Najeriya (CBN), ya rage farashin dalar Amurkar da yake sayar wa mutane daga N375 zuwa N360.
A wani sako da bankin ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, ya ce zai fara sayar wa bankuna dala akan Naira 357 inda su kuma bankunan kasar za su fara sayar wa ga mutane kan Naira 360.
Babban bankin yana shiga kasuwar kudaden kasashen wajen ne domin rage gibin da ke tsakaninta da ta bayan fage.
KU KARANTA: Shekara 2 ina rokon Buhari ya tsaya takara - Elrufa'i
A watan da ya wuce dai kasuwar bayan fagen na sayar da dala kan N520 bayan babban bankin Najeriya ya rage darajar naira zuwa 375 ga dala daya.
An sayar da dala N315 a hukumance a ranar Litinin.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng