Lauyoyi 3 da suka fi kowa kudi duk Najeriya
A Najeriya dai burin kowane yaro ya zama Likita ko Injiniya ko kuma Lauya. Sai dai ba kowa ke samun wannan damar ba. Yanzu Legit.ng sun kawo maku jerin Lauyoyin da su ka fi kowa kudi a kasar:

1. Tunde Folawiyo
Duk Najeriya ba Lauyan da ya kai Tunde Babatunde Folawiyo arziki. Ko da yake ba Lauya bane kurum yana kuma kasuwanci don shi ne Darektan MTN a Najeriya. Mujallar Forbes tace Folawiyo ya mallaki sama da dala miliyan 650.

2. John Olatunde Ayeni
John Ayeni mai kusan shekaru 50 a Duniya Lauya ne wanda yana taba kasuwanci yana cikin masu kudin kasar gaba daya. John Ayeni ya rike bankin nan na Skye Bank shekaru sama da 10 da suka wuce. Ayeni ya ba Naira dala miliyan 600 baya.
KU KARANTA: Sakataren Gwamnati yace bai aikata wani laifi ba
3. Adewumi Ogunsanya SAN
Mista Ogunsanya babban Lauya ne a Najeriya wanda yana cikin ‘yan autan manyan Lauyoyi. Ogunsanya yana daga cikin manyan bankin nan na Heritage. Shakka babu ya mallaki sama da Dala miliyan 250.

Akwai kuma dai wasu Attajiran Lauyoyin irin su Barista Jimoh Ibrahim wanda ya fito takarar Gwamnan Jihar Ondo kwanaki, Aare Afe Babalola, Wole Olanipekun, Gbenga Oyebode da dai sauran su.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Gwamna ya tuka matar sa a mota
Asali: Legit.ng