Abun tausai: Uwa ta hadu da danta shekara 7 bayan rikicin Boko Haram ya raba su (Hotuna)
- Kungiyar Red Cross ta mika wani yaro mai shekaru 7 ga iyayansa a jihar Borno, bayan ta gano shi a sansanin 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Nijar.
- Rikicin Boko Haram wanda aka kwashe shekaru da dama ana fafatawa, ya raba mutane da dama da iyalansu, musamman kananan yara da mata a yankunan Arewa maso gabas.
Mahaifiyar Musa ta bayyana farin cikinta da sake yin ido hudu da danta bayan ta debe tsammanin ganin shi a duniyar nan.
KU KARANTA: Buhari zai kara fadada harkar sufurin jirgin kasa a Arewa
A wani labarin kuma, Wata Mata a Kudancin Myanmar ta maka danta a kotu bayan ya kira ta da sunan Karuwa tare da yada hutunanta a shafin facebook saboda yana adawa da wani sabon saurayinta.
A ranar Talata ‘Yan sanda suka cafke yaron mai suna Wana Oo dan shekaru 21 bayan mahaifiyarsa mai suna Tin Tin Hla ta tuhume shi da cin mutuncinta a Facebook.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng