Wani katon asara ya cewa uwar sa 'karuwa', matakin da ta dauka zai baka mamaki (Karanta)
Wata Mata a Kudancin Myanmar ta maka danta a kotu bayan ya kira ta da sunan Karuwa tare da yada hutunanta a shafin facebook saboda yana adawa da wani sabon saurayinta.
A ranar Talata ‘Yan sanda suka cafke yaron mai suna Wana Oo dan shekaru 21 bayan mahaifiyarsa mai suna Tin Tin Hla ta tuhume shi da cin mutuncinta a Facebook.
‘Yan sandan Myanmar sun ce matar ta kai karar yaron a Kotu wanda ya karba laifin da mahaifiyarsa ke tuhumarsa.
KU KARANTA: An dakatar da wani basarake saboda fyade
Wana Oo zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari karkashin dokar da ta haramta cin mutuncin wani a kafofin sadarwa na zamani.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na ganin dokar ta sabawa ‘yancin fadin albarkacin baki.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng