An kama muguwar uwa, bayan tayi ma danta mugun duka sannan ta binne shi a cikin sirri (HOTO)

An kama muguwar uwa, bayan tayi ma danta mugun duka sannan ta binne shi a cikin sirri (HOTO)

Yan sandan jihar Ogun sun kama wata matar aure mai suna, Bisola Olukoya kan zargin kashe dan ta mai shekaru 16.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, jami’in kula da huldar jama’a na hukumar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwa al’amarin a ranar Juma’a, 24 ga watan Maris, cewa wacce ake zargin ta aikata laifin a garin Onifade-Itele dake jihar.

An kama muguwar uwa, bayan tayi ma danta mugun duka sannan ta binne shi a cikin sirri (HOTO)
Bisola Olukoya

“Hukumar yan sandan jihar ta kama wata Misis Bisola Olukoya dake gida mai lamba 40, unguwar Ifelodun Onifade Itele, kan laifin dukan danta mai shekaru 16 Toheeb Olukoya har lahira,” inji kakakin hukumar yan sandan.

KU KARANTA KUMA: Wayyo! Ana nema a kashe ni Inji Hadiza Bala Usman

Oyeyemi ya kara da cewa, al’amarin ya afku ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Maris. Yace wacce ake zargin, yayinda ta ke dukan marigayin, ta buga masa wani katako a kai, wanda yayi sanadiyan mutuwar yaron. Sannan kuma, mai laifin ta yi saurin binne marigayin sannan kuma ta gudu ta bar gidan.

Kakakin yan sandan yace a lokacin da labara ya iso hukumar yan sandan, jami’in dan sanda a sashin Itele, Lukmon Adejumo, ya jagoranci jami’an tsaro don bincike sannan daga baya suka bi sahun mai laifin inda aka ka,a ta a Iyana Ipaja a Lagas.

Ya ce kwamishinan yan sanda, Ahmed Iliyasu, ya bada umurnin tura mai laifin zuwa sashin bincike na jihar. Ya kuma roki jama’a da su dunga tsare fushin su musamman a lokacin gyara yankin su.

KU KARANTA KUMA: Yadda muka gano dukiyoyin Alex Badeh – EFCC

Kalli wani bidiyo a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel