Wayyo! Ana nema a kashe ni Inji Hadiza Bala Usman
Shugabar Hukumar NPA ta kasa ta koka inda take cewa wasu Jama’a na nema su ga bayan ta. A wannan makon ne dai Hajiya Hadiza Bala Usman tayi wannan kukan
Hadiza Bala Usman mai shugabantar hukumar NPA masu kula da iyakokin ruwa ta bayyana cewa wasu na nema su batar da ita. Hajiya Hadiza ta bayyana wannan ne a shafin ta na Twitter a Ranar Laraba.
Hajiya Hadiza Bala tayi aiki da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i a matsayin shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnati kafin shugaba Buhari ya nada ta shugabar Hukumar NPA na kasa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aika takarda kasar Ingila
Wata Jarida dai tayi ikirarin cewa shugabar ta NPA ta gana da wasu ‘Yan Jam’iyyar APC a baya. Sai dai tayi maza ta karyata wannan zargi inda tace za ta kai kara kotu. Tuni dai masu jaridar su ka nemi ayi masu afuwa amma tace sam sai a gaban Alkali don kuwa an bata mata suna.
Haka kuma Femi Falana wanda shararren Lauya ne a Najeriya ya bayyana cewa Majalisar dattawa na da damar bada umarni a kama Sakataren Gwamnatin kasar Babachir David Lawal. Falana yace doka ta ba Sanatocin wannan damar idan har Babachir bai hallara gaban ta ba.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng