Muhimman sirruka 5 Na ‘kokunba’ masu ban mamaki

Muhimman sirruka 5 Na ‘kokunba’ masu ban mamaki

Cucumber tana da sirruka da dama a tattare da rayuwar dan adam, domin masana kiwon lafiya sun bayar da umarnin a yawaita yin amfani da ita saboda irin sirrukanta a jiki.

Kadan daga cikin amfaninta ga rayuwarmu ta yau da kullum sun hada da.

Muhimman sirruka 5 Na ‘kokunba’ masu ban mamaki
Muhimman sirruka 5 Na ‘kokunba’ masu ban mamaki

1. Narkar Da Kitse

Duk mai yawan amfani da Cucumber zai rika samun isasshen lafiya, karin ni’imar jiki da kwarjini. Wannan ta sa mata suke yawaita sanya barinta a kan idanuwansu. Dalili a fili ne cewa a daidai lokacin da mace ta sanya Cucumber a kan fuskarta, Cucumber za ta tsotse duk rubabben kitse da ke tattare a kan fatar kwayar idanunta nata, domin tana da wasu sinadaran da ke warkar da irin wadannan cutukan na kan fata. Ba ma a fatar idanu kawai ba, an nuna cewa mutum zai iya gyara Cucumber ya dora kan duk inda yake masa ciwo, ko inda fata ta sami matsala. Sannu a hankali komai zai gushe kuma zai samu waraka nan take.

2. Ciwon Kai

A duk lokacin da mutum ya sha wahalar aiki ko gajiyar musamman, wadanda ke haddasa nauyin jiki a lokacin da aka tashi daga bacci, muddin ya dan ci Cucumber kafin ya kwanta, zai tashi tamkar wanda ya wuni yana motsa jiki.

KU KARANTA: An gano sirrin Buhari wajen yakar Boko Haram

3. Warkar da Warin Baki

Da yawa daga cikin mutane suna fama da matsalar warin baki. Muddin za su yi magana bakinsu ya rika wari ainun ta yadda ba za a so matsawa kusa da su ba. Idan kina da wannan matsalar kawai ki bare Cucumber, ki sanya a cikin bakinki sai ki rike shi a daidai saman bakin da harshe kimamin Sakan 30. Daga nan ki tofar da ita a kasa. Idan kika luzumci wannan, warin bakinki zai kau ba tare da bata lokaci ba.

Muhimman sirruka 5 Na ‘kokunba’ masu ban mamaki
Muhimman sirruka 5 Na ‘kokunba’ masu ban mamaki

4. Karin Kuzari

A duk lokacin da gajiya ta yi miki yawa, maimakon kwanciya don ki huta, kawai ki yanka Cucumber ki ci kadan, za ki wartsake nan da nan.

5. Gyara Fatar Fuska

Ina masu amfani da mayuka masu lalata fuska ko bata jiki? Da zarar zarar kin yayyanka Cucumber kika dora a wuta ya tausa sosai, kawai ki bude marfin tukunyar sai ki sanya fuskarki don dumin ruwan ya shafi fuskarki. Daga nan za ki ga yadda fuskarki za ta koma ba tare da wata matsala ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng