Ka ji abin da ake hada Lemun Coca Cola da shi?

Ka ji abin da ake hada Lemun Coca Cola da shi?

Kwanan nan Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana iya shan lemun nan na Coca Cola sai dai wani Dan Majalisa ya bayyana abin da ake hada lemun da shi

Ka ji abin da ake hada Lemun Coca Cola da shi?
Ka ji abin da ake hada Lemun Coca Cola da shi?

Honarabul Gudaji Kazaure mai wakiltar Kazaure/Gwiwa/Roni/’Yankwashi a Majalisar wakilai ta tarayya ya bayyana abin da ake hada lemun nan na Coca Cola wanda ake kira Coke da shi. Dan Majalisar ya bayyana haka ne a Majalisa jiya.

A wani Bidiyo da ke yawo a shafin Youtube kamar yadda aka saba gani don kuwa Dan Majalisar ba bako bane wajen magana game da harkokin da su ka shafi kasa ya bayyana cewa da ruwan rijiya ake hada lemun Coca Cola.

KU KARANTA: Madalla: Dala ta fara saukowa kasa

Ka ji abin da ake hada Lemun Coca Cola da shi?
Honarabul Gudaji Kazaure ya tona asirin Coke?

Dan Majalisar yace irin lemun Coke din da ya saya a Kaduna ya sha bam-bam da wanda ya saya a kasar Jamhuriyyar Nijar. Honarabul Gudaji yace ba mamaki da ruwan rijiyar birtsatsai da wasu sinadari ake hada lemun da mutane suke sha.

Gudaji Kazaure yayi kira da Hukumar NAFDAC da SON su dauki mataki wajen duba irin wadannan lemun sai dai Hukumar kula da lafiyar magunguna da abinci watau NAFDAC da kuma Hukumar SON mai tabbatar da nagartar kaya a kasar tayi wani binciki inda ta gano cewa babu wata matsala wajen shan wannan lemu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng