YANZU YANZU: Anyi jana’izan yan kasuwa 22 da suka mutu a mummunan hatsarin mota

YANZU YANZU: Anyi jana’izan yan kasuwa 22 da suka mutu a mummunan hatsarin mota

- An rahoto wani hatsari da ya afku a jihar Kebbi

- Hatsarin yayi sanadiyan mutuwar yan kasuwa 22

- An gudanar da jana’izan wadanda hatsarin ya cika da su

An gudanar da jana’izan wasu yan kasuwa 22 da suka mutu a mummunan hatsarin mota a hanyar Tunga Giwa-Ruwa dake karamar hukumar Shanga na jihar Kebbi.

YANZU YANZU: Anyi jana’izan yan kasuwa 22 da suka mutu a mummunan hatsarin mota
YANZU YANZU: Anyi jana’izan yan kasuwa 22 da suka mutu a mummunan hatsarin mota

Hatsarin ya afku ne lokacin da wata doguwar mota kirar Toyota da tayi kokarin afkawa rami ta daki wani dan achaba sannan ya hanbare, inda ya kashe dan achaban da fasinjoji 22 dake motar.

Vanguard ta ruwaito cewa mataimakin Gwamna Bagudu na gwamnatin Shanga, Alhaji Garba Salihu, ya fada ma Gwamna Atiku Bagudu cewa yan kasuwar na dawowa daga kasuwar Tungan Giwa ne lokacin da al’amarin ya faru.

KU KARANTA KUMA: Majalisar wakilan Najeriya ta gargadi shugaba Buhari kan wa’adin mulki

Salihu yace motar ya fada cikin wani rami ne sannan ya kama da wuta.

Yace mutane 22 ne suka mutu a take a inda hatsarin ya afku, yayinda takwas suka ji raunuka sannan kuma an dauke su zuwa babban asibitin Yauri. Bagudu, wanda ya kai ziyara inda abun ya afku, ya bi sahun sallar jana’izan da akayi ma wadanda abun ya cika da su, wanda aka binne a babban kabari.

Ya taya wadanda suka tsira jimami sannan kuma yayi alkawarin daukar nauyin kudin asibitin su sannan kuma ya ci gaba da basu taimako.

A wani al’amari makamancin wannan, an rahoto cewa wasu daliban jami’ar Baze guda uku sun mutu a wani mummunan hatsarin mota.

A cewar wani rubutu a shafin Instagram daga Instablog9ja, wasu daliban jami’ar Baze guda uku sun mutu a wani mummunan hatsarin mota.

KU KARANTA KUMA: An gano Fayose yana cin shinkafa a gidan abinci na kan hanya

An bayyana sunayen daliban da suka mutu a matsayin, Umar Rahamaniya, Sadiq da kuma Mashkur Tambuwal, a hanyar su ta zuwa makaranta a ranar, 21 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel