Wata ta haukace da gane mijin ta ashe gawa ne

Wata ta haukace da gane mijin ta ashe gawa ne

- Grace bata san cewa Tony gawa ne, sai da wani dangin shi ya shigo gida da hotunan Tony na da, sai kuma yana gaya mata cewar ya mutu tun shekaru 11 can baya

- Wasu sun yi ƙoƙari su kira Tony a waya, wasu sun je ofishin shi amma basu taradda shi ba domin bai tafi wajen aiki a ranar ba

Wata ta haukace da gane mijin ta ashe gawa ne
Wata ta haukace da gane mijin ta ashe gawa ne

Zahiri wata ta samu kwancecen kai da ta gane mijin da take aure da shi ya riga yam utu tun shekara 2002. Ta gane wannan bayan ta haifi yara 2.

Misis Grace Amadi, ta na aure ta kuma haifu ma gawa wadda ya mutu tun shekara 2002.

Yadda rahoto ya nuna, Grace ta aure Mista Tony tun shekara 6, kuma sun yi zaman lafiya da shi. Sun haifi yara 2 duka mata a shekara 2011 da 2013. Sun yi zama a bakin ruwa a garin Fatwakal jihar Ribas. Tony na tafiyan aiki kowani rana.

Grace bata san cewa Tony gawa ne, sai da wani dangin shi ya shigo gida da hotunan Tony na da, sai kuma yana gaya mata cewar ya mutu tun shekaru 11 can baya.

Grace ta fara hiwu tana kuka, ta ki ta yarda, tana fushi, ta ji tsoro tana ta jefar da kanta a kasa domin ta ba ma kanta raoni. Maƙotan ta suka fito ganin mai ke faruwa.

Yadda Maƙotan suka ce, hotuna da dangin Tony ya kawo; 1 ya nuna shi yana bikin aure da wata a shekara 2000 ga watan Mayu. Akwai wadda kuma yana cikin hatsarin mota wajen da ya mutu, akwai wadda Tony na cikin akwatin gawa ana yimishi Jana'izan a shekara 2002, na karshe hotunan shi ne na ƙabarin shi da suna shi da ranar da aka haife shi da kuma ranar da ya mutu.

Wasu sun yi ƙoƙari su kira Tony a waya, wasu sun je ofishin shi amma basu taradda shi ba domin bai tafi wajen aiki a ranar ba.

Yanzu an tafi da Grace wani coci domin a yi mata adua, yaran ta kuma suna wajen Maƙotan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: