Barayin shanu da yan daba sun mika kai ga hukuma
Akalla bindigogi 1000 ne wasu yan daba, masu kora shanu da yan banga suka sallamar a shirin da gwamnatin jihar Zamfara da sashe soja 1 ta shirya.
A wata jawabin da kakakin hukumar soji, Kanal Sani Usman Kukusheka, ya saki yace gwamnatin jihar da hukumar soji na aiki domin samar da zaman lafiya.
An samu rikice-rikicen satan shanu da kuma hare-haren Fulani makiyaya amma hukumar soji ta lashin takobin smaar da zaman lafiya.
KU KARANTA: Melaye da Aduda sun bayar da cin hanci akan Magu
Yace: “ Shirin sallamar da makaman yan daba, masu kora shanu, da yyan banga da gwamnatin jihar Zamfara da hukumar sojin sashe 1 a shirya ta haifi da mai ido yayinda an sallamar da makamai da yawa a kananan hukumomin Gusau, Maru da Anka a jihar Zamfara.
Makaman da aka samu sune ; Bindigar AK-47 uku, 2G3, Bindiga mai carbi 1, kokon barkonon tsohuwa 1, barkonon tsohuwa 3, bindigogin gargajiya 690, kananan bindigogin gargajiya 192,….".
Gwamnatin jihar da hukumar soji tana kokarin tattaunawa da masu uwa da tsaki domin samar da zaman lafiya.
https://www.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng