Mahaifina na bani N500 a duk lokaci da ya kwana da ni – yar shekara 15 ta koka
A ranar Alhamis, 16 ga watan Maris, wata yarinya mai shekaru 15 dake cike da kunci ta bayyana yadda mahaifinta mai shekaru 42, ke bacci da ita da ‘ya’yarta tun lokacin da mahaifiyarsu ta bar gidan shekaru 2 da suka wuce.
Yarinyar bata ce mahaifinta na bacci da ita a duk sanda ya ga dam aba amma ta ce yana bata N500 a duk sanya yake so ya kwanta da ita. A cewar jaridar Vanguard, hukumar yan sandan Ketu sun kama mutumin mai suna, I.D Idowu bayan makota sun kai karan al’amarin ga hukumar yan sanda.
An rahoto cewa, matar wanda ake zargin ta bar gidan auran ta shekaru biyu da suka wuce lokacin da ta gano cewa mijinta na kwana da ‘yarsu mai shekaru 17. Amma sai mijin ya nace kan cewa lallai ta bar gidan ba tare da ko daya daga cikin yara ukun da suka haifa ba, dukkan su mata, wanda shekarun su yake 17, 13 da ‘yar shekara takwas.
KU KARANTA KUMA: An kama dan Boko Haram kurma kuma bebe dauke da wayoyi 8
Vanguard ta tattaro cewa babban ‘yar ta kasa jure ma cin zarafin, don haka ta bar gidansu na Ketu, inda ta bar kannenta da kaddarar su. Yar idowu ta biyu tayi zarge shi da bata naira dari biyar (N500) a duk lokacin da yake son kwana da ita.
Asali: Legit.ng