Wata budurwa mai ɗauke da cutar ƙanjamau tana neman miji ruwa a jallo

Wata budurwa mai ɗauke da cutar ƙanjamau tana neman miji ruwa a jallo

Wata tsaleliyar budurwa ta aika ma shugaban kamfanin jaridar ‘Zambian Observer’ doguwar wasika inda ta bukace shi daya taimaka mata ta samu mijin aure, don kuwa tsohon mijinta ya rasu. Amma fa tana da ciwon kanjamau.

Wata budurwa mai ɗauke da cutar ƙanjamau tana neman miji ruwa a jallo
Muchanka

Matar mai suna Sharon Haabantu Munachaka, mai shekaru 31 ta rubuta wasikar nata kamar haka:

KU KARANTA: Yaƙi da cin hanci da rashawa: “Kada ka tausaya ma ɓarayin gwamnati” - Obasanjo ga Buhari

“A yanzu dai ni malamar lissafi ce a wata makaranta dake lardin Choma, a shekarar data gabata ne na kammala karatun digiri a jami’ar UNZA, kuma a yanzu ina karatun digiri na 2.

“Sai dai an gano ina dauke da kwayar cutar kanjamau ne bayan mutuwar tsohon mijina, wanda shine ya harbe ni da ita sakamakon biyebiyensa. A yanzu ina neman miji kowane iri ne da zai taimake ni ya aure ni duk da halin da nake ciki, ban damu ba ko yana da kanjamau ko bashi da shi.”

Munachaka ta karkare wasikar ta da cewa “Zan yi farin ciki idan zan samu miji kirista, kuma mai bin koyarwar addinin sau da kafa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel