Ranar haihuwar shararren dan wasa Ali Nuhu

Ranar haihuwar shararren dan wasa Ali Nuhu

Shahararren dan wasan Kwaikwayon nan Ali Nuhu ya cika shekaru 42 da haihuwa a Duniya. Ali Nuhu dai ba karamin tauraro bane, amma shin wai wanene Ali Nuhu?

Ranar haihuwar shararren dan wasa Ali Nuhu
Ranar haihuwar shararren dan wasa Ali Nuhu

A jiya ne shahararren dan wasan Hausa Ali Nuhu ya cika shekara 42 da haihuwa. An dai haifi Ali a Ranar 15 ga Watan Maris na shekarar 1974. Mahaifin Ali Nuhu mutumin Gombe ne yayin da Mahaifiyar sa kuma ta fito daga Yankin Borno.

Ali Nuhu yayi fina-finai masu yawan gaske inda ya lashe kyaututtuka a sanadiyar wasu. Ali ya fara fim ne tun shekaru sama da 15 da suka wuce. Ali Nuhu dai ba wasan kwaikwayon Hausa kadai ya tsaya ba, ta kai yana yin fina-finan Ibo na Nollywood, dama can Ali yana jin turanci radau har da yaren Hindu.

Ranar haihuwar shararren dan wasa Ali Nuhu
Ranar haihuwar shararren dan wasa Ali Nuhu

KU KARANTA: Kotu ta ce za a bar Musulmai su shiga Amurka

Ranar haihuwar shararren dan wasa Ali Nuhu
Ranar haihuwar shararren dan wasa Ali Nuhu

Ali Nuhu yana auren Hajiya Maimuna Garba Ja Abdulkadir kuma suna da ‘ya ‘ya biyu wanda yanzu daya daga cikin su yake fitowa a shirin fim. Ali Nuhu ya fito a fina-finai kusan 300 daga shigowar sa fagen.

Ali dai har kwas yayi a sha’anin fim a Kasar Amurka. Jama’a da dama suna yi masa kallon jarumi sai dai wasu ba su jin dadin irin abin da yake aikatawa a fina-finan sa na Nollywood. Ali dai ya cika shekaru 42 a Duniya jiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel