Sheikh Mabera ya yi alwashin kai wani fasto kotu domin danganta Yesu Almasihu da Allah

Sheikh Mabera ya yi alwashin kai wani fasto kotu domin danganta Yesu Almasihu da Allah

Wani malami addini musulunci Sheikh Hussaini Yusuf Mabera, ya yi barazanar kai wani mashahuri faston Najeriya kotu.

Sheikh Mabera ya yi alwashin kai wani fasto kotu domin danganta Yesu Almasihu da Allah
Sheikh Mabera ya yi alwashin kai wani fasto kotu domin danganta Yesu Almasihu da Allah

Wani malami addini musulunci Sheikh Hussaini Yusuf Mabera, ya yi barazanar kai wani mashahuri faston Najeriya T.B. Joshua kotu.

Malamin ya yi wannan bayyani a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa ta Facebuk, inda ya zargi faston da yawan kwatanta Yesu Kiristi a matsayin Allah.

Malamin addinin na cewa ya sha kallo tashar talabijin na Emmanuel TV, amma ya na mamaki dalilin da ya sa faston danganta Yesu a matsayin Allah a gaban dubban sauraro.

Sheikh Mabera ya ce bayan wasu binciken littafai addini, littafi mai tsarki kansa yana da yawa shaida wanda ya saba da imani cewa Yesu Kristi Allah ne.

Malamin ya yi iƙirarin cewa fasto Joshua da kuma sauran kiristoci sun kazance masu karanta littafi mai tsarki ba tare da fahimtar abin da suke karanta ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel