Al’ummar jihar Ribas sun yi ma shugaba Buhari addu’a

Al’ummar jihar Ribas sun yi ma shugaba Buhari addu’a

Jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Ahoad da gabas na jihar Ribas sun gudanar da taron addu’o’i ga shugaban kasa Muhammadu Buhari don cigaba da samun sauki.

Al’ummar jihar Ribas sun yi ma shugaba Buhari addu’a
Chibudum Nwuche a hannun hagu

Masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun yi amfani da wannan dama wajen sake jaddada goyon bayansu ga daya daga cikin shuwagabannin jam’iyyar daya fito daga yankin nasu Prince Chibudom Nwuche, saboda jajircewar sa da iya tafiyar da jam’iyyar.

Taron addu’ar ya gudana ne a gidan Nwuche a kauyensu mai suna Ochigba, inda magoya bayan jam’iyyar suka yaba masa sakamakon sadaukarwa da jajircewa dayake nunawa wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar a kowane mataki.

KU KARANTA: Hukumar ƙidaya zata yi ƙididdigan ýan Najeriya a 2018

Shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Ahoada, Owuze Umah ya gode ma yayan jam’iyyar saboda samun daman halartar taron addu’an da suka yi ma shugaban kasa a yayin tafiyansa birnin Landan, kuma ya shawarce su dasu cigaba da addu’ar.

Al’ummar jihar Ribas sun yi ma shugaba Buhari addu’a
Al’ummar jihar Ribas sun yi ma shugaba Buhari addu’a

Sa’annan ya yaba musu saboda kokarinsu wajen ganin jam’iyyar ta kara karfi a jihar, kuma ya bukaci da a hada kai, a zama tsintsiya madaurinki daya don taran zabukan dake karatowa a jihar da ma kasa gaba daya.

Umah ya yaba ma Nwuche saboda kokarinsa wajen tabbatar da ganin jam’iyyar a karamar hukumar tana gudanar da tarukanta a kai a kai, tare da samar da hanyoyin cigaban jam’iyyar.

Yayin dayake nasa jawabinn, Nwuche ya bukaci yayan jam’iyyar dasu daina tunanin samun wani abu tun yanzu, maimakon haka, ya shawarce su dasu dage wajen bada gudunmuwa ga jam’iyyar don samun nasarori.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng