Matan Chibok: An bar hannun Boko Haram ba a koma gida ba

Matan Chibok: An bar hannun Boko Haram ba a koma gida ba

A watan Afrilun 2014 aka sace ‘Yan mata sama da 200 daga wata Makaranta da ke Garin Chibok a Jihar Borno. Ko ya rayuwar wadannan mata ke kasancewa bayan sun bar hannun Abubakar Shekau?

Matan Chibok: An bar hannun Boko Haram ba a koma gida ba
Wasu matan Chibok kenan bayan su kubuta daga hannun Shekau

Makonni kadan bayan sace matan na Chibok aka busa kakakin BBOG masu neman Hukuma ta gano inda matan suke, ko da dai tun kafin nan an sace mata bila-adadin. Kawo yanzu dai an gano kusan 20 daga cikin ‘Yan matan na Chibok da aka saka lamba.

Tun bayan da aka sace wadannan ‘Yan mata dai aka fara kuwwar cewa a gano su, daga nan ne ‘Yan Boko Haram suka fahimci cewa sun yi babban kamu; Hakan har ta sa aka fara karrama ‘Yan matan Chibok dabam da sauran ‘Yan mata Inji wasu daga cikin ‘Yan matan da aka kama har su ka auri ‘Yan ta’addan. Kai wata tace har bayi aka ce ta zaba cikin sauran matan.

KU KARANTA: Aljanu sun fatattaki shugaban kasa daga fadar Gwamnati

Matan Chibok: An bar hannun Boko Haram ba a koma gida ba
Matan Chibok: An bar hannun Boko Haram ba a koma gida ba

Da alamu dai Gwamnati ta biya ‘Yan ta’addan wani abu kafin a saki wasu daga cikin ‘Yan matan. Kungiyar nan ta Red Cross ta Duniya da Gwamnatin kasar Switzerland ne suka shiga cikin yarjejeniya da ‘Yan Boko Haram. Bayan an saki yaran dai iyayen su sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Sai dai fa har yanzu wadannan yara ba su dawo gida ba, don kuwa suna nan boye a wani wuri inda ake kokarin kara jirkita tunanin su daga abin da suka ci karo da shi a baya hannun ‘Yan Boko Haram. Yanzu dai wata tace sau biyu kurum ake bari suyi waya da iyayen su a mako inda aka saka su a wata Makaranta. Sai lokacin hutun Kirismeti ne kadai dai aka bari yaran suka gana da iyayen su, wanda hakan ba ya masu dadi.

Legit.ng Hausa suka fassara wannan daga Jaridar NY Times ta Amurka

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel