Ba zamu taba hada kai da masu zagin sahabbai da matan Annabi (SAW) ba - Shugaban Izalah

Ba zamu taba hada kai da masu zagin sahabbai da matan Annabi (SAW) ba - Shugaban Izalah

A wata tattaunawa da majiyar mu tayi da Shugaban kungiyar Izalatul Bid’a wa ikamatus sunnah na kasa,Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana muhimmanci hadin kai tsakanin musulmi, amma ya ce su a Izala ba za su taba hada kai da masu zagin Sahabban Annabi da Matansa ba.

Sheihin ya bayyana hakan ne lokacin da aka tambayeshi ko wadanne hanyoyi ya kamata a bi don ganin al’ummar musulmi sun hada kai, duk da bambance-bambancen da ke tsakani a Nijeriya?

Sai ya kada baki yace: "Babu shakka hadin kai abu ne mai muhimmanci a addinin musulunci, shi ne ma jagora, domin Allah ya umarci Annabi Muhammad (SAW) ne da hada kan al’umma, kamar yadda sauran Annabawa suka yi. Domin Manzon Allah ya ce addinin nan zai kasu kashi wajen 73. Cikin wadannan hanyoyi, hanya daya ce da za ta kai musulmi ga tsira gobe kiyama. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce hanyar kawai da za ta kai ga tsira ita ce, ku rike littafin Allah da Sunnata."

KU KARANTA: Ban taba yin irin wannan mummunar rashin lafiyar ba - Buhari

Sai ya ci gaba da cewa: "Akwai haduwar Yahudawa, za ka gansu kansu a hade, amma zukatansu daban-daban suke. To Allah ya ce kada mu yi irin wannan haduwar. Wuri daya ne Allah ya ce mu yi koyi da Yahudu, wurin kuma shi ne wurin hadin kai. Domin Allah ya ce Kafiran nan masoyan juna ne, suna rufa wa junansu asiri. Don haka Allah ya ce ku ma Muminai ku yi irin wannan, idan ba ku hada kanku ba za a sami barna a bayan kasa."

"Saboda haka akwai kungiya (RABIDA), wadda ke hada kan musulmin duniya baki daya. Wadanda ba a tafiya da su a wannan kungiya su ne wadannan mutane da suke zagin Sahabban Manzon Allah da iyalan gidansa. Babu yadda za a yi masoyin Annabi ya zagi matan Annabi. Babu yadda za a yi masoyin Annabi ya zagi Sahabban Annabi, wadanda ta hanyarsu aka samo Addinin. To akwai ’yan Shi’a, wadanda suka mayar da akidarsu la’anta ga Sahabbai da Matan Annabi. Saboda haka ba yadda za a yi mu hada kai da su, har sai ranar da suka janye wannan la’antar, sannan su dawo cikinmu." A cewar tasa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng