‘Aljanu da fatalwa’ sun fatattaki shugaban ƙasa daga fadar gwamnati

‘Aljanu da fatalwa’ sun fatattaki shugaban ƙasa daga fadar gwamnati

Shugaban kasar Brazil Michel Temer ya danganta dalilinsa na fita daga fadar gwamnatin kasar ga wasu miyagun aljanu da suka addabe shi a fadar gwamnatin kasar.

‘Aljanu da fatalwa’ sun fatattaki shugaban ƙasa daga fadar gwamnati
shugaba Michel Temer

Kamar yadda jaridar kasar Brazil ta ruwaito, Temer ya baiwa al’ummar kasar mamaki a lokacin daya sanar da barinsa fadar gwamnatin kasar tare da uwargidarsa da karamin yaronsa mai shekaru 7.

Shugaban kasar ya koma gidan mataimakin shugaban kasa dake kusa da fadar shugaban gwanmatin kasar.

KU KARANTA: Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya

Ita dai katafariyar fadar shugaban gwamnatin kasar Brazil hamshakiyar fada ce, sunanta ‘Alvorada’ kuma tana da katafaren kwamin wanki, filin kwallo, coci, asibit da filin shakatawa.

‘Aljanu da fatalwa’ sun fatattaki shugaban ƙasa daga fadar gwamnati
Fadar gwamnati

Amma shugaban kasa Temer mai shekaru 76, tare da matarsa Marcela 33 sun guji fadar saboda wasu al’amura dayace bai gane “Ina jin wani banbarakwai haka, tun ranar da na shiga gidan ban iya bacci ba” inji shugaban kasar.

Jaridar ta cigaba da fadin, ita ma uwargidar shugaba Temer tana jin irin wannan matsala, sai dai yaronsu ne Michelzinho ne kadai da bai san meke tafiya ba, don kuwa ko a jikinsa, zaka hange shi yana guje gujensa

‘Aljanu da fatalwa’ sun fatattaki shugaban ƙasa daga fadar gwamnati
‘Aljanu da fatalwa’ sun fatattaki shugaban ƙasa daga fadar gwamnati

“Har ma na fara jin kamar ko dai aljanu ne?” inji Gwamnan. Jaridun kasar sun bayyana cewar shugaban kasar har malamai ya dauko don su kori aljanun, amma abin yaci tura.

Wannan yasa Temer ya koma fadar mataimakin shugaban dake kusa da fadar gwamnati, mai suna Jabaru.

Shugaba Temer ya hau kujerar mulki ne dai bayan majalisar dokokin kasar sun tsige tsohuwar shugabar kasa Dilma Rousseff sakamakon badakalar kasafin kudi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel