Matar mawaƙin shugaba Buhari, Rarara ta haihu, an samu Buhari
Uwargidar shahararren masoyin kuma mawakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Adamu wanda aka fi sani da Rarara ta haihu a ranar Asabar, 11 ga watan Maris.
Rarara da kansa ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda yace ‘Ku taya mu murna, Allah ya azurta ni da namiji, a ranar Asabar. Allah ya raya shi, tare da sauran yayan musulmai gabaki daya.”
KU KARANTA: “Zan sake komawa nan bada daɗewa ba don a ƙara duba ni” – inji Buhari
Rarara dai mawaki ne wanda yayi suna a Arewa musamman wajen rera wakokin siyasa, inda ko a dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kasar Birtaniya sai daya rera wata waka data karbu a tsakanin mutanen kasar nan wanda yayi ma taken “Sannu da sauka baba Buhari”.
A baya ma dai Rarara yayi wakar ‘masu gudu gudu’ bayan shugaban kasa Buhari ya lashe zaben shugaban kasa.
Shi dai Rarara dan asalin jihar Kano ne, kuma ya smau karuwan ne kwana daya bayan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga birnin Landan inda ya kwashe kwanaki 50 yana duba lafiyarsa.
A wani labarin kuma, Rarara ya kaddamar da sabuwar wakarsa a garin Malumfashi inda ya halarci taron murnan maraba da dawowar shugaban kasa Buhari.
Sai dai majiyoyi da dama sun bayyana cewar Rarara ya sanya ma jaririn da aka haifa masa suna Buhari.
Allah ya ja zamanin Buhari, kuma Ya raya Buhari.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng