An kashe Fulani Makiyaya 2 a kudancin Kaduna
- An kashe Fulani Makiyaya 2 a kudancin Kaduna, jihar Kaduna
- Makiyayan yan shekaru 14 da 20 ne
- An harbesu har lahira ne yayinda suke kiwo awakansu
An samu wani tashin hankali a jihar Kaduna yayinda aka kashe Fulani makiyaya guda 2 a ranan Asabar, 11 ga watan Maris.
Wannan abu da ya faru ya tayar da hankalin mutane a yankin. An harbesu har lahira yayinda suke kiwo a Anguwan Yashi, karamar hukumar Jema’a.
KU KARANTA: Burata bai isa ya hana Biafra ba- MASSOB
Game da cewar jaridar Premium Times, Ibrahim Abdullahi, mataimakin sakataren kungiyar Miyetti Allah, yace wadanda aka kashe sune Anas Shuaibu, 20, da Yahaya Musa, 14.
Kana Malam Abdullahi yayi kira ga jama’ar Fulani kada su dau fansa su bari hukuma tayi aikinta saboda a samu zaman lafiya a yankin.
Aliyu Othman, kakakin hukumar yan sanda wanda ya tabbatar da labarin yace hukumar yan sanda na cikin gudanar da bincike cikin al’amarin kuma an rigaya da damke mutane 9 masu alaka da kisan.
https://www.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng