Tonon silili: Asirin wani Fasto na cigaba da tonuwa

Tonon silili: Asirin wani Fasto na cigaba da tonuwa

Wata Budurwa mai suna Stephaine Otobo na cigaba da da fallasa asirin wannan shararren Faston mai suna Apsotle Johnson Sulaiman na cocin 'Omega Fire'.

Tonon silili: Asirin wani Fasto na cigaba da tonuwa
Tonon silili: Asirin wani Fasto na cigaba da tonuwa

Idan ba a manta wannan Faston nan da ya taba kiran Mabiyan sa da su kashe Fulani Makiyaya ba har yanzu dai wannan Faston yana cikin ruwan zafin gaske. Wata Budurwa ce dai ta ke tona asirin irin huldar da suka yi a baya.

Stephaine tace Faston ya taba daukar ta zuwa Kasar Italiya inda aka yi wani taro a Garin Napoli ya kwana da ita. Budurwar dai ta bayyana yadda Faston ya rika bata makudan kudi domin ya kwanta da ita, ta kuma ce idan karya take yi tana da shaida.

KU KARANTA: An gano gidan buga kudi a Kebbi

Otobo ‘Yar Kasar Cananda ta bayyana yadda Faston ke zuwa dakin ta tun safiyar asuba a wancan lokaci na makonni biyu. Bugu-da-kari dai Stephaine tace tana da hotunan banza da Faston ya rika turo mata a wancan lokaci.

Budurwar tana karar wannan babban Limami bayan da tace ya yaudare ta inda yayi mata karyar zai aure ta ya rika lalata da ita. Faston dai ya bugawa wannan Budurwa ciki ya kuma tsere ya bar ta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel