Gungun ýan bindiga da dama sun miƙa wuya ga sojoji a Zamfara, sun ajiye makamai masu yawa
Wasu gungun yan bindiga tare da barayin shanu sun mika wuya tare da mika makamansu ga dakarun rundunar sojan kasa a jihar Zamfara, kamar yadda Kaakakin rundunar Sani Usman ya bayyana.
Birgediya janar SK Usman ya bayyana cewa tubabbun yan bindigan sun mika wuya ne biyo bayan wani shirin afuwa da gwamnatin jihar tare da hedikwatar runduna ta daya na Sojoji suka faro tun a shekarar 2016.
KU KARANTA: Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia
Sanarwar tace: “A ranar Laraba 8 ga watan Maris 2017,wasu tubabbun yan bindiga tare da yan-sakai daga kauyen Ruwan Tofa, ‘Yar Galadima da Babban Doka dake karamar hukumar Maru, da wasu daga kauyen Danwaren na karamar hukumar Tsafe da kuma kauyen Mada dake karamar hukumar Husau sun mika dimbin miyagun makamai ga rundunar sojan kasa.
“Cikin makaman da suka mika akwai bindigun AK-47 guda 3, kananan bindigu guda 323, bindigan toka guda 1,169, bindigan revolver guda 54, bindiga mai baki biyu guda 22, sai kuma wasu bindigu masu baki uku guda 102.
“An mika makaman ne a hannun bataliya ta 223 a gaban wasu jami’an gwamnatin jihar tare da shuwagabannin hukumomin tsaro da dama. A yan watannin da suka gabata, an samu makamai sama da 1000 da aka mika su ga hukuma.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng