Na gaji da zaman aure, mijina ya sake ni in koma Karatu – Inji Fatima Baba

Na gaji da zaman aure, mijina ya sake ni in koma Karatu – Inji Fatima Baba

- Wata matan Aure ‘yar shekara 17 ta bukaci hukumar kare hakkin yara kanana na jihar Neja da ta raba aurenta da mijinta saboda tana bukatar komawa makaranta domin ci gaba da karatunta

- Yarinyar mai suna Fatima Baba, tace zaman aure ya isheta , makaranta ta ke so ta koma

Na gaji da zaman aure, mijina ya sake ni in koma Karatu – Inji Fatima Baba
Na gaji da zaman aure, mijina ya sake ni in koma Karatu – Inji Fatima Baba

Iyaye nane suka auradda ni ga mijina Salisu Mohammed dan shekara 35 wanda na dauka zan iya zama dashi. Amma yanzu gaskiya bana son sa kuma bana kaunar zaman aure saboda haka nake kira da a warware auren domin karatu nake so in koma yanzu.

Salisu Mohammed yace babu wani abu da ya hada shi da matarsa, suna zaman lafiya kwatsam sai ta nuna zaman ya isheta wai karatu ta ke so ta koma.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu! Buhari ya karbi bakuncin wani babban abokin sa

Yace daga farko bayan auren nasu matarsa Fatima tana jin dadin zaman auren kuma basu sami wata matsala ba.

Bai san mene ya faru ba yanzu ta ce ta gaji da zaman auren wai araba shi saboda tana so ta koma makaranta.

Dakacin garin Shaba, Halilu Shaba ya koka da yadda ake aurar da yara ba tare da suna son auren ba.

Yace bai kamata anayi wa mata auren wuri ba.

Shugaban hukumar Maryam Kolo tace mata suyi koyi da irin nuna jarumtar da Fatima tayi domin kwato ma kanta hakkin na so ta koma makaranta.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng