Hawaye ya kwaranya yayinda malamin katolika da malamin musulunci suka rungume juna a Minna (Hotuna, Bidiyo)
Ya kasance bankwana mai taba zuciya ga mutanen Minna, jihar Niger sakamakon ritayan Reverend Jeremiah O’Connell.
Hawaye ya kwaranya yayinda malamin musulunci Sheik Ahmed Lemu da Pada O’Conell sukayi bankwana da junansu.
Sheik din ya rungume O’Connell na tsawon mintuna 3, inda yake masa godiya ga dukkan abubuwan da yayi ma mutanen Najeriya, musamman mutanen garin Minna.
Wannan al’amari mai taba zuciya ya afku ne a tsakanin malaman addinan guda biyu a daidai lokacin da ake fuskantar tsana mai tsanani tsakanin addinan guda biyu a kasar.
Kalli bidiyon a kasa:
A cewar mutanen, ya taba rayukan mutane da dama sannan kuma bazasu taba mantawa da ayyukan alkhairi da yayi masu ba.
An nada ma Pada O’Connell sarauta a matsayin JAGABAN Ilimin Mai Martaban Minna.
Yayi aiki a matsayin shugaban makarantar Gwamnati a Minna tsawon shekaru 50
Sakamakon ritaya da yayi, zai koma Ireland.
Asali: Legit.ng