Labari cikin hotuna: Gwamnan Bauchi ya kai ziyara inda ake hakan man fetur a Bauchi
A jiya ne Laraba, 8 ga watan Maris, Gwamnan Jihar Bauchi, Barista Mohammed A. Abubakar, ya kai ziyaran gani da ido wajen ake tonon man fetur a karamar hukumar Alkaleri dake jihar Bauchi.
Wani makarancin jaridar Legit.ng ya bamu rahoton cewa gwamnan jihar, Barista Mohammed Abubakar ya kai ziyarar ganin ido inda ake hakan man fetur a karamar hukumar Alkaleri na jihar Bauchi.
KU KARANTA: An kaiwa Olisah Metuh hari
Idan baku manta ba Shekaran da ya gabata, Shugaban kamfanin man fetur na kasa wato NNPC, Dakta Kachalla Maikanti Baru, ya tabbatar da cewa an samu man fetur a a cikin daya daga cikin rijijoyin da ake gudanar da aiki a kusa da Yankari Game Reserve.
Mun samu wanda labari da hotuna ne daga Ahmadu Manage Bauchi.
Kalli sauran hotunan:
https://twitter.com/naijcomhausa
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
Asali: Legit.ng