Kun ji irin makaman yakin da ake kerawa a Najeriya? (Hotuna)
- Babban sifeton 'yansandan Najeriya Ibrahim Idris ya nuna jin dadinsa tare da yabawa kan yadda ma'aikatar kera kayan yaki dake Ode Remo a jihar Ogun take gudanar da ayyukanta
- Alhaji Ibrahim Idris yayi yabon ne lokacin da ya ziyarci ma'akatar domin ganewa idanunsa yadda ma'aikatar ke gudanar da ayyukanta
Yace muna jin dadi da kwazon 'yan Najeriya wanda bashi da iyaka kuma ana iya ganin abun da 'yan kasar ke iya yi. Yace 'yan Najeriya sun yi nisa da fasaha da cigaba.
Ibrahim Idris yace ma'aikatar ta kera kayan yaki tana taimakawa wajen samarda aikin yi ga matasa da inganta tattalin arzikin kasa da kuma bunkasa harkokin tsaron kasa.
Shi ko mai kula da ayyukan ma'aikatar Mr. Ayo Omotoriowo yace kamfanin ya samarwa masu aikin tsaron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kayan aiki irin su motoci masu sulke a kasashen Afirka ta Tsakiya da Sudan ta Kudu. Kana gwamnatin kasar Ruwanda ta sayi motocin yaki daga ma'aikatar. Yace ma'aikatar na iya gasa da duk wata ma'aikatar sarafa kayan yaki irinta a duniya.
Masanin tsaro Ade Ogundeyi yace a yau ma'aikatar nada nagartar kera motocin yaki da kayan yaki har ma wadanda a da can muna neman kayan yaki a wurinsu, yanzu a wurinmu suke nema, inji shi.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng