Sarkin Bauchi ya dakatar da Wazirinsa bisa wannan dalili

Sarkin Bauchi ya dakatar da Wazirinsa bisa wannan dalili

-Mai martaba Sarkin Bauchi ya dakatar da Wazirinsa kuma tsohon mai ba shugaba Obasanjo shawara kan ayyuka na musamman a bisa rashin nuna da'a da kin bin ummarni

-An dai samu dan sabani tsakanin Sarkin da Wazirinsa ne a masallacin Juma kan wurin zama a inda Sarkin ya fifita Walin Katagum a cewar mata majiya.

Sarkin Bauchi ya dakatar da Wazirinsa bisa wannan dalili
Sarkin Bauchi ya dakatar da Wazirinsa bisa wannan dalili

Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu ya ba da umarnin dakatar da wazirinsa Muhammadu Bello - Kirfi daga harkar masautar jihar

Sarkin ya bayar da umarnin dakatarwar ce a ranar Litinin 6 ga watan Maris shekarar 2017, ta hanyar wata sanarwa daga fadar sarkin.

Duk da cewa sanarwar ba ta bayar da ta takamaiman laifin da Wazairin ya aikata ba a cewar jaridar The Daily Sun, sai dai sanarwar ta dai ce kawai an Sarkin ya dakatar da shi ne nan take kuma babu ranar dawowa a bisa "rashin nuna hali nagari da kuma kin biyayya ga masarautar jihar".

Sai dai wata majiya na cewa, wata 'yar rashin fahimta ce da ta faru a masallacin Juma'a tsakanin Sarkin da wazirin dakuma Walin Katagum ce ta haddasa dakatarwar.

Majiyar ta cigaba da cewa, a ranar Juma'a 3 ga watan Maris ne na shekarar 2017 a yayin sallar Juma'a, Wazirin ya ja da Sarki bayan da Sarkin ya nuna a bar Walin katagum ya zauna a wurin da Waziri ke zama a sahun Sallar wanda hakan bai yiwa Wazirin dadi ba.

"A lokacin da Waziri ya shigo masallachin sai ya ga Walin Katagum Alhaji Adamu Aliyu tsohon Jakadan Najariya a kasar Japan zaune kusa da sarki wanda nan ne wurih

"Ganin cewa ba yi daidai ba, sai Waziri ya nunawa Wali hakan tare da neman ya tashi daga wurin. Shi kuma sarki ya daga hannunsa mai nuni da cewa ya kyale shi".

"Wannan a cewar majiyar, ita ta sa Wazirin ya fadawa sarki a take a wuirn cewa, wurinsa ne kuma hakan da sarki yayi zai kawo raini ga masarauta".

Majiyar ta kuma ci gaba da cewa, hakan daga dukkanin alamu bai yiwa Sarki dadi ba. Sakamakon hakan ne Sarkin ya ba da umarnin dakatar da Wazirin nan ta ke kuma na din-din-din. Domin a nuna masa iyakarsa.

Muhammadu Bello - Kirfi ya taba rike mukamin mai ba shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman a zamanin mulkin Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: