Da magani a gonar yaro: Dabino da kuma fa'idarsa ga lafiya jiki

Da magani a gonar yaro: Dabino da kuma fa'idarsa ga lafiya jiki

Dabino dan itace ne da al'umma da dama suka san shi, abu ne mai daraja masamman ma da ya ke ya kumshi kusan duk abincin da dan adam ya ke bukata. Ga wani bincike da Baban Manar da Abu Unaisa suka yi donmin amfanin jama'a

Da magani a gonar yaro: Dabino da kuma faidarsa ga lafiya jiki
Da magani a gonar yaro: Dabino da kuma faidarsa ga lafiya jiki

Dabino na da tsohon tarihin da wasu 'ya'yan bishiyan ba su da shi, ba wai yanzu ba ko tun a da can mutane sukan dauke shi a matsayin abinci, za kuma a iya cewa yana gaban duk wani dan itace, masamman sabo da sukarin da ya tattara a cikinsa, wannan zakin ya shafi busasshe da danye wanda ya nuna.

Wata malama mai zurfin ilimi a bangaren kayayyakin abinci a Juddah, wato Prof. Waddaha Mohammed na cewa, Cin kwayan dabino guda goma mai nauyin 100g zai iya ba mutum wasu abubuwa na amfani ga lafiya jiki.

Haka ma hukumar kula lafiya ta Amurka ta bayar da shawara ga matasa da cewa, wanda ya ke cin dabino zai sami duk abin da ya ke bukata na Magnesium, Manganese, Copper, zai sami kusan abin da yake bukata na rabin sinadaran Potassium da calcium.

Ana kimanta zakin sukarin da dabinon ya tattara wajen kashi 78-70 cikin dari na abubuwan da dabinon ya kumsa, kuma wannan sukarin na dabino nan take ya ke narkewa a cikin jini sabanin sauran 'ya'yan bishiya.

A nan ne za mu ga hikimar muslunci ta sanya dabino ya zama abin farko da mai azumi zai fara ci, wannan don a dawo masa da abubuwan bukatar da ya rasa ne cikin gaggawa, Allah Mai girma ne a dukkan lamarinsa.

Ba wannan kadai ba akwai ma 75g na carbohydrate, 63g na sukari, 8g na Dietary fiber, 0.4g na Fat, 2.5g na Protein, 21g na ruwa,0.262 mg na Manganese, 1.32 na minerals.

Abin da Prof. Waddaha ta ce shi ne bushasshen dabino ya qumshi: Carbohydrate 79.6%, Fat 2.5%, Water 33%, Minerals 1.32%, Dietary fiber 10%, sai Vitamins A, B1, B2 da C, kamar yadda ya kuma ya kumshi abubuwa da dan dama, a takaice in ka duma dabino shi kadai ya isa ya zama abincin da zai gina jiki in ba don tsoron a yi masa cin koshi ba.

Bincike ya nuna cewa dabino ya kumshi sanadaran; Minerals da Calcium, da Protein, da Fat, da Lime, da Coramine, da Dietry fiber, da Phosphor, da da Chlorine, Manganese, da Potassium, da Copper, da Vitamin C, da kuma Magnesium.

Da wannan ne za mu gane cewa dabino ya kumshi manya-manyan abubuwa na abinci, wadanda za su gina jiki da jijiya, suma bayyana wa mutum matasantarsa ko da kuwa ya dan kwana biyu, da za a haga dabino da madara tabbas abinci ne mai kyawun gaske, masamman ga wanda yake da matsalar ciki.

Masana kimiyya na cewa, abubuwan gina jiki da su ke cikin danino na daidai ne da na wani nau'i na nama, ko ribi uku na kifi.

Kuma ya kan amfanar da masu cutar fatarar jini, da wasu cututtuka da suka shafi kirji kamar yadda ake kwaba shi a dafa a rika sha daidai gwargwadon yadda aka nunawa mutum.

Dabino na amfanar da kananan yara, da matasa, da 'yan wasa, da ma'aikata, da ramammu, da kuma mata masu ciki.

Dabino ya kan taimakawa masu matsalolin ido gaba daya, kamar dai yadda ya ke taimakawa wajen kara gani, da kara karfin kunne, haka na kuma ya kan sa wa mutum natsuwa tare da yi masa maganin saurin fushi ko yawan fada da mutane. Shi ya sa ake son mutum ya nike shi ya hada da madara ya sha da safe.

Dabino kan tausasa jijiyoyi masu dauke da jini, ya gyara uwar hanji, sannan ya yi mata maganin radadi da rauni, ya na kuma taimakawa kwakwalwa sosai ba kadan ba, kamar dai yadda ya kan taimakawa maza wajen ba su kuzarin shimfida.

Dabino ya na taimaka wa masu azumi da tsaffi masu yawan shekaru, ya kan kuma taimaka wajen nike abincin da aka ci, ya ba mutum yin fitsari sosai don fitar da cuta, ya tsarkake masa hanta, ya wanke masa koda, nikakkensa kuwa ya kan yi maganin tari, da majina.

In aka kara masa kwakwa da madara a lokaci guda ya kan kara masa qarfin aiki ba shakka, abu ne mai kyau matuka.

Da wadannan bayanan za ka fahimci cewa komai amfanin dabino a matsayin abinci, a gefe guda kuma magani ne.

Sau dai yawaita cinsa ba tare da ka'ida ba zai iya haifarwa mutum da abubuwa da dama, ko in utum yana da wata cutar ya tayar masa ita.

Ga wani nau'in abincin da zai amfane ka

Asali: Legit.ng

Online view pixel