Amina Mohammed ta yi magana mai mai ratsa jiki a jawabin ta na farko a majalisar dinkin duniya
Tsohuwar ministar muhallin Buhari daga jihar Adamawa kuma sabuwar mataimakiyar Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya tayi wani dogon bayani mai rasta jini a jawabin ta na farko a majalisar.
An dai ruwaito cewar Amina Muhammad ta yi bayain ne mai cike da hikima da basira a cikin satin da ya gabata yayin da take shan rantsuwar kama aiki a majalisar.
A cikin jawabin nata, Amina Muhammad wadda ta fito daga arewacin Najeriya tace dole ne majalisar ta dinkin duniya ta shirya tsaf kuma tayi adalci idan dai har tana so a rika daratta ta.
KU KARANTA: Sabon sako daga Osinbajo
Hakama ta jinjinawa Sakataren na majalisar saboda yadda da yayi da ita yayin da kuma ta sha alwashin ba mara da kunya a aikin nata.
Mai karatu dai zai tuna cewa, Sakatare-Janar na majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya nada Ministar muhalli ta Najeriya Amina Mohammed a matsayin mataimakiyarsa.
Mista Guterres ya kuma nada wasu mata biyu a wasu manyan mukamai a majalisar.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng