Jirage 35, yan rakiya 1,455; Karanta yadda sarkin ke facaka da kudi yayin tafiya
- Sarkin Saudiyya ya ziyarci kasar Indonesiya a karon farko da wani Sarki na kasar ya yi irin ta cikin shekaru 47
- A yayin da ziyarar tasa, wadda ta kasuwanci ce zuwa kasar da ta fi ko wacce yawan Musulmai a duniya ke daukar hankali, haka ma dan hutun da zai yi a tsibirin Bali, da irin kayan alatun da zai tafi da su ke kara daukar hankalin jama'a
Sarki Salman dan Abdul Aziz al-Saud ya isa birnin Jakarta tun ranar Laraba, a wani bangare na wata ziyara da yake yi ta tsawon wata guda a wasu kasashen yankin Asiya, da suka hada da Malesiya, da Brunei, da Japan, da China da kuma Maldives.
Wakilin majiyar mu a Indonesiya Christine Franciska, ya yi duba kan yadda mutanen kasar suke ta sha'awar ziyarar sarkin.
Kafofin yada labarai na Indonesiya sun bayar da rahoton cewa sarkin ya taho da kayayyakin da nauyinsu ya kai ton 459, wadanda suka hada da motoci kirar mercedes-Benz S600s guda biyu, da kuma lifta mai aiki da lantarki guda biyu.
KU KARANTA: Ana shirin kafa sabuwar PDP
Wani kamfanin jirage da aka dora wa alhakin dakon kayayyakin sarkin mai suna"Jasa Angkasa Semesta" ya shaida wa kafar yada labarai ta Antara cewa an sauke ton 63 na kayan a Jakarta, yayin da za a kai sauran ton 396 na kayan tsibirin Bali.
Tawagar tasa ta hada da mutum 620 'yan rakiya, da wakilai 800 wadanda suka hada da ministoci 10 da kuma 'ya'yan sarki 25.
Kamfanin ya kara da cewa jirage 27 ne za su yi jigilar tawagar sarkin zuwa birnin Jakarta, sannan kuma jirage tara su dauke su zuwa tsibirin Bali.
Duk da cewa dai an san Sarakuna da shugabannin kasashe sun saba tafiye-tafiye da kayayyakin alatu tare da babbar tawaga, to amma mutanen Indonesiya na ganin alfahari ya yi yawa a wannan ziyarar.
Wani mai amfani da shafin Twitter ya rubuta cewa, "Da yawan 'yan Indonesiya suna ganin cewar sarkin Saudiyya ya nuna fariya sosai a wannan tafiya. Ni dai na fi alfahari da shugaban kasarmu Jokowi saboda saukin kansa."
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng