Dandalin Kannywood: Mawaka na fafukar a sako Saddiq zazzabi
-Masu sana'ar shirya finafinai da wasu mawaka sun soma fafutukar ganin an sako Sadiq Zazzabi wanda wata kotun tafi-da - gidanka ta sa a tsare shi saboda wakar Kwankwaso
-Kotun ta sa a tsare matashin mawakin ne kafin ta yanke hukunci bayan ya saki wakar ba tare da izinin hukumar tace finafinai ta jihar ba
Masu shirya finafinai, da masu sana'ar waka a jihar Kano, da wasu jihohi na arewa sun soma fafutukar ganin an sako Sadiq Ahmad wanda aka fi sani da Sadiq Zazzabi wanda wata kotun tafi da gidanka a Kano ta sa a tsare.
Tsarewar ta sa ta biyo bayan fitar da wata waka ce da hukumara tace finafinai ta jihar ta ke zarginsa da sakia gari ba tare da izininta ba.
Wakar wacce yabo ce ga tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa kwankwaso, wanda a yanzu dangantaka tsakaninsa da gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje ta ya tsami, ita ake zargin ta haifarwa da matashin matsala.
'Yan Fim din da wasu fitattaun mawaka sun rika daukar hotuna dauke da takarda mai dauke da rubutun cewe a sako mawakin suna kuma sa wa a dandalin sada zumunta na Facebook da Instagram.
Cikin fitattun mawakan da suka shiga sahun masu neman sakin mawakin sun hada Fati Nijar da Abubakar Ladan Amin ALA da TY Sha'aban da sauransu.
Tuni dai tsare mawakin ta janyo ka-ce-na-ce a ciki da kuma wajen jihar baya ga cewa, magoya bayan tsohon gwamnan kuma sanata a yanzu, na zargin matsi da muzgunawa a jihar tun bayan da Ganduje ya karbi mulkin.
Hakan ta sa majalisar dattijai ta umarci babban sifeton 'yan sanda da ya gurfana a gabanta kan batun gallazawa 'yan kwankwasiyyar a makon jiya
Asali: Legit.ng