Karshen tika-tika tik: An sa ranar shari’ar Sambo Dasuki
Kotu ta sa ranar da za ayi shari’a da tsohon mai bada shawara game da harkar tsaro Sambo Dasuki. Ko ya za a kaya?
Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a Birnin-Tarayya Abuja ya saka ranar da za a zauna game da shari’ar Sambo Dasuki tsohon mai bada shawara game da harkar tsaro a lokacin shugaban kasa Jonathan Goodluck.
Alkali Baba-Yusuf ya sa shari’ar a ranar 16 ga watan Maris dinnan watau dai nan da makonni biyu kenan. Ana dai ta jira a ga ko ya za a kare tsakanin Dasuki da kuma Hukumar EFCC. Lauyan Dasuki, Ahmed Raji SAN ya nemi dai dage karar zuwa nan gaba.
KU KARANTA: DSS ta damke wani Dan adawar Buhari
Ana dai zargin Sambo Dasuki da laifuffuka kusan 22 wadanda suka hada da karkatar da kudin makamai na sama da dala Biliyan 2 ya karkaar lokacin da ya ke rike da ofishin mai bada shawara kan harkar tsaro a mulkin Shugaban Kasa Jonathan Goodluck.
Femi Falana SAN Lauyan shugaban kungiyar IMN Ibrahim Az-Zakzaky, ya rubuta wasika ga Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo SAN game da cigaba da daure malamin. Falana yace idan har gwamnati ba ta saki Zakzaky ba zai dauki mataki babba.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng