Yadda jirgin sama da ke tafiya Yola ya lallace – Medview
- Fasinjoji da za su tafi Abuja sun bi wani jirgi daban a dai dai karfe 4:30 na rana
- Amman an tabbatar musu cewar babu damuwa, jirgin zai tafi
- Allah ne ya taimake su 105 fasenja da taya jirgin Boeing 737 ta ‘Air Peace din da taya ya fashe da za su tashi a filin Murtala Muhammed na Legas
A ranar Talata Febwairu 28, wani jirgin sama na Medview na tafiya daga Legas zuwa Yola ya lallace sai aka fasa tafiya bayan direban jirigin ya lura da wani laifi tare da jirgi.
Mai magana da yan labarai kamfani jirgin Medview, Obuke Oyibhota ya ce jirgin na kan tafiya a hanyar kasa na filin Murtala Mohammed a Legas, da aka gane da laifin.
Oyibhota ya ce:
“Abin ya faruda rana ne. Jirgin bai dawo bai yi tafiya ba, yana kan taka kan titi filin jirgi ne sai Kaftain ya gano cewar, wajen da yake zaman tuki ya yi zafi.
“Da ya tafi ne da jirgin, da wajen ya koma sanyi ama bai yi aka ba domin ya hana hatsari, sai ya dawo wajen ajiyewa na jirgin.
“Abin da ya faru kenan kuma kowa bai ji ciwo ba. Jirgin na kasa ana duba a gane mai ya kawo akan nana.”
KU KARANTA: Direbobin tanka sun hallaka yan Najeriya akalla 1,000 cikin wata daya - FRSC
Domin aka da ya faru, su mutane 100 da suka shiga jirgin, an ke su wani jirgi daban su cigaba da tafiyan su.
Ya kuma cewar, abin da direban jirgin ya yi ya yi dai dai da kaidan (SARPs)
‘Standards and Recommended Practices ta ‘(ICAO) ‘International Civil Aviation Organisation’
A yadda aka ce, Oladejo Olowu daya daga cikin fasenja din ya ce an ke su gidan hutu a Legas.
Ya kuma ce fasenja da za su tafi Abuja sun bi wani jirgi daban a dai dai karfe 4:30 na rana. Sai kuma nasu na Yola aka kai karfe 8:30 na safe’ian Laraba.
Inji Olowu, wai ko su ma sun gane akwoi damuwa da jirgi mai lamba VL 2102, kafin ya yi niyar tashi.
Ama an tabbatar musu cewar babu damuwa, jirgin zai tafi. Ya ce Allah ne ya taimake su 105 fasenja da taya jirgin Boeing 737 ta ‘Air Peace din da taya ya fashe da za su tashi a filin Murtala Muhammed na Legas.
Asali: Legit.ng