Tsohon shugaban Najeriya ya jagoranci yin addu'a ga Buhari

Tsohon shugaban Najeriya ya jagoranci yin addu'a ga Buhari

Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun lafiya, tsohon shugaban kasar Janar Yakubu Gowon, ya nuna damuwarsa game da yadda ake saka siyasa a rashin lafiyar shugaban kasa.

Tsohon shugaban Najeriya ya jagoranci yin addu'a ga Buhari
Tsohon shugaban Najeriya ya jagoranci yin addu'a ga Buhari

Gowon wanda ya jagoranci addu’o’i na musamman don ci gaban Najeriya, a jahar Adamawa, ya bukaci yan ‘kasar musamman yan siyasa da suke karatun ta natsu domin ciyar da kasar gaba.

A cewar tsohon shugaban shima lokacin da yake kan mulki yayi rashin lafiya, kuma hakan ba wani abu bane na damuwa domin kowa kan iya kamuwa da rashin lafiya a kowanne lokaci.

KU KARANTA: An gano cutar dake damun Buhari

Gowon ya kuma yi kira ga duk ‘yan Najeiya da a ci gaba da yiwa shugaban addu’a, duk da yake likitoci suna bashi kulawar da ta kamata, da kuma gujewa cece-kuce irin na siyasa.

Sai dai kuma wannan ziyarar addu’oin da tsohon shugaban kasar ya jagoranta na zuwa ne yayin da hadakar kungiyar magoya bayan Buhari da Osinbajo ta BOA, ke gudanar da gangamin addu’o’a a Yola, inda aka yi wa shugaba Buhari addu’a ta musamman.

Dan Majalisar Dokokin jihar Adamawa, Rufai Gombi, na daga cikin shugabanin kungiyar BOA, yace sun shirya taron gangamin addu’ar ne don rokon Allah ya baiwa shugaban lafiya ganin ayyukan da aka fara musamman a jahohin Arewa maso Gabashin kasar.

Ya zuwa yanzu dai ana cigaba da gudanar da irin wadannan addu’o’i ga shugaba Buhari a wasu sassan Najeriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel