Majalisar Dinkin Duniya: ‘Yar Najeriya ta kafa tarihi

Majalisar Dinkin Duniya: ‘Yar Najeriya ta kafa tarihi

Kwanakin baya ne Majalisar Dinkin Duniya ta dauke Ministar Buhari, yanzu haka har an rantsar da ita a matsayin mataimakiyar shugaban majalisar a Birnin New York da ke Amurka.

Majalisar Dinkin Duniya: ‘Yar Najeriya ta kafa tarihi
‘Yar Najeriya ta kafa a UN

Majalisar Dinkin Duniya watau UN ta rantsar da ‘Yar Najeriyar nan kuma tsohuwar Ministar kasar Amina J. Mohammed jiya a matsayin mataimakiyar shugaban majalisar a ofishin Majalisar da ke Birnin New York na kasar Amurka.

Shugaban Majalisar Antonio Gutierrez ne da kan sa ya rantsar da Amina Muhammad inda yace suna mai matukar farin ciki da ta shigo cikin tafiyar ta su. Jim kadan bayan rantsar da Amina ta shiga gudanar da wani aikin tare da bayyana muradun ta. An bude ofishin mataimakin shugaban majalisar ne shekaru 10 da suka wuce.

KU KARANTA: An rantsar da Ministar Buhari

Majalisar Dinkin Duniya: ‘Yar Najeriya ta kafa tarihi
Majalisar Dinkin Duniya: ‘Yar Najeriya ta kafa tarihi

Antonio Gutierrez wanda ya zama Shugaban Majalisar na 9 a Tarihi, ya nada Amina J. Mohammed a matsayin Mataimakiyar sa tun watan Disamba sai dai ba ta fara aiki ba sai kawo yanzu saboda tana rike da ofishin Minista a Najeriya inda ta ke kokarin kammala wasu ayyuka.

Amina ce dai ‘Yar Afrika ta biyu a tarihi da ta taba rike wannan matasayi a Majalisar dinkin Duniya. Amina Muhammad ta zama wata abin koyi ga matasa masu tasowa. Tun ba yau ba dai ta fara aiki da Majalisar dinkin Duniyar watau UN ta kuma taka rawar-gani.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng