Dokar Trump kan musulmi: An wulakanta dan Muhammad Ali a filin jirgin sama

Dokar Trump kan musulmi: An wulakanta dan Muhammad Ali a filin jirgin sama

- Jami`an shige da fice sun tsare shi tare da yi masa tambayoyi saboda kasancewarsa musulmi

- Camacho Ali na dawowa ne daga taron wani taron tuna tarihin bakaken fata a Amurka a suka halarta shi da mahaifiyarsa a Jamaica

- Hana shiga Amurka da Donald Trump ya yi, ya tilastawa musulmi fuskantar matsanancin bincike a filayen jirgin sama a Amurka.

Jami`an shige da fice a Amurka sun tsare dan Muhammad Ali a filin jirgin saman Florida inda su ka yi masa tambayoyi game da asalinsa da addininsa duk da cewa ya bayyana kansa a matsayin da, ga marigayi Muhammad Ali.

Dokar Trump kan musulmi: An wulakanta dan Muhammad Ali a filin jirgin sama
Dokar Trump kan musulmi: An wulakanta dan Muhammad Ali a filin jirgin sama

A cewar jaridar The Times, wani makusancin iyalin Muhammad Ali wanda ya yi magana ranar Asabar ya ce Jami`an a filin jirgin sun kara matsa masa yayin da ya ce shi musulmi ne.

Camacho Ali na dawowa ne daga taron taron tuna tarihin bakaken fata a Amurka 'Black History Month' a Jamaica shi da mahaifiyarsa Khalilah Camacho Ali.

An jawo su gefe, aka kuma raba su da juna yayin da su ke zuwa wurin binciken masu shige da fice ranar 7 ga watan Fabrairu a filin jirgin saman kasa da kasa na Fort Lauderdale-Hollywood.

Chris Mancini, wata makusanciya kuma lauya ta ce, sai da danta ya nuna hotonta da tsohon mijinta sannan aka sake shi. Dan na tsohon zakaran dan wasan damben duniya, Muhammad Ali dan shekara 44 wanda, ya tabbatar da cewa shi musulmi ne an tsare shi kimanin sa`a biyu duk da cewa ya fadawa Jami`an cewa shi dan Muhammad Ali ne kuma dan kasar Amurka, a cewar Mancini.

Karo na farko kenan da aka taba tambayar Ali da mahaifiyarsa ko su musulmai ne yayin shiga Amurka.

"Abu ne a fili cewa abin da ya jawo wannan tambayoyi shi ne sunan Larabawa da ya ke da shi da kuma addininsa."

"Yayin da ake tsare da shi, an dinga tambayar Ali game da asalinsa da sunansa, "kamar tambayar fara gabatar da shiri," Mancini ya fada.

Camacho Ali da Ali su na zaune ne a Florida. Tun sannan ba su fita daga Amurka ba kuma su na shirin kai kara gaban kuliya.

Zakaran damben duniya marigayi Muhammad Ali wanda ya lashe kanbin har sau uku kuma mai gabatar da ayyuka irin na jin kai, ya mutu a watan June na shekarar bara yana da shekara 74 bayan dadewa da ya yi yana fama da cutar karkarwar jiki.

A watan Disamba 2015, ya fitar da wani jawabi inda ya ce:

"Mu musulmai ya kamata mu tashi tsaye mu yi maganin wadanda ke amfani da musulunci don biyan bukatunsu."

Yana daya daga cikin shahararrun `yan wasanni na shekara 100 da su ka wuce, BBC ta nada shi a matsayin dan wasan karni

Ga ra'ayin jama'a kan shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel