Inda ranka! Miji ya taya matar sa murnar ta haifar masa 'shege' (Hotuna)
-Inda ranka zaka sha kallo a duniyar nan don kuwa abun mamaki baya karewa.
-Wani hoto ne ya rika yawo na wasu ma'aurata yan kasar Zambiya da suka dauka tare da dan su mai kama da yan kasar Sin.
- Matat tana aiki ne agidan wani dan kasar Sin
Wani hoto dauke da ma'aurata miji da mata bakaken fata yan kasar Zambiya da dan su farar fata mai kama da yan Chana yana ci gaba da ba mutane al'ajabi.
KU KARANTA: Zafin kishi ya jefa wata cikin halaka
Ma'auratan masu suna Fabio Phiri da kuma Priscilla Phiri sun dora hoton ne a kafar sadarwa inda suke godewa Allah da dan da suka samu.
Wani abun mamaki da yake ciki shine ita matar tana aiki ne a gidan wani dan kasar Sin a kasar ta Zambiya.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng