Kudurin dokar hana karin aure ba gudu ba ja da baya

Kudurin dokar hana karin aure ba gudu ba ja da baya

- Mai martaba sarkin Kano Muhammadu sunusi na II ya jaddada matsayinsa kan kudurin dokar da za ta taikata karin yin aure ga masu karamin karfi.

- Kudurin dokar ta janyo ka-ce-na ce a ciki da wajen kasar dangane da takaita auren da kuma yawaitar mata da kuma irin fitinar da hakan za ta haifar.

Kudurin dokar hana karin aure ba gudu ba ja da baya
Sarkin Kano da matansa uku tare da wasu daga cikin 'ya' yansa

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya jaddada matsayinsa kan kudurin dokar da za ta taikata karin yin aure ga masu karamin karfi da cewa babu gudu babu ja da baya ganin yadda mata ke cin bakar wahala a hannun wasu mazaje.

A wata hira da Sarkin ya yi da wata 'yar jarida Sa'adu Ahmed Legit.ng ta kuma yi arba da kofen hirar, Mai martaba sarkin yayi bayanin tanade-tanaden dokar da hujjojinsa daga kur 'ani da kuma Hadisi

Mai martaba sarki a hirar ya ce, kwamiti ya kafa na manyan malamai wadanda suka zauna a kwamitance suka kuma duba matsalar suka kuma yi fitar da rahoto, wanda da shi ne za a fitar da doka.

Wasu daga cikin tanade-tanaden kudurin dokar kamar yadda 'yar jaridar ta rawaito sun hada

Ta tabbatar wa da 'ya mace baliga 'yancin ta zabi mijinta kuma ta haramta ayi wa ya baligha auren dole ba da iznint ba.

Sannan auren karamar yarinya sosai sai da iznin alkalin shari'a wanda zai yi shawara da likitoci, ya kuma tabbatar da maslahar yarinyar ce kuma larura amma ba haka kawai zi kau ba.

Kudurin dokar ta kuma haramta dukan mace, duk kuwa wanda ya yiwa matarsa rauni akwai Qisaasi ko Diyya kamar yadda shari'a ta tanada.

Sannan kudurin ta tabbatar da hakkin ciyarwa, da tufatarwa, da muhalli, da lafiya da kuma idan mutum na da hali ya ki yi, to alkali zai umurce shi yayi, Idan ya ki yi Alkali na da ikon ya kwace dukiyarsa a ciyar da iyalinsa, alkali zai iya ma daure shi kamar mai bashi.

Sannan duk wanda zai auri mace fiye da daya akwai sharudda a cikin littattafan mazhaba, ciki har da ba za a hada a gida daya ba, sai idan su suka yarda su zauna haka.

Bugu da kari a cikin kudurin dokar dai akwai kyautatawa mace da dukiya idan an sake ta, da kuma hakkin kula da duk dan da aka haifa.

Sannan da akwai kuma maganar halaccin tazara tsakanin yara da amfani da hanyar jinkirta haihuwa wacce ba ta sabawa shari'ar addinin musulunci ba.

Tun lokacin da sarkin ya bayana wannan kudurin doka ya janyo ce-ce-ku-ce daga ciki da kuma wajen jihar.

Hoton bidiyon zanga-zangar goyon bayan shugaba Buhari da aka yi a Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel